Contact Info

Nasiharmu ta Yau Juma’a Daga Bakin Alhaji Mustapha A Sani Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Kamar kowacce Juma’a a wannan rana mai albarka Shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Alhaji Mustapha A Sani ya sake mika sakon barka da Juma’a ga al’ummar Musulmi.

Mustapha A Sani ya bayyana cewa ya kamata mutum Musulmi ya daina shiga abin da bai shafe shi ba wato abin da babu ruwansa a ciki.

“Ina kira ga mutane da su daina shiga abin da bai shafesu ba, domin wasu mutanen suna tafka kuskuren shiga abin da babu ruwansu kuma hakan kuskurene. Domin akwai Hadisi guda da yayi magana akan hakan da yake cewa: Yana daga cikin kyawun Musuluncin mutum da ya rabu da abin da bai shafe shi ba”.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya yi addua’ar Allah ya bamu albarkacin wannan rana ta Juma’a mai albarka.

Send:

Leave a Reply