Contact Info

Nasihar Yau Juma’a Daga Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

A wannan rana ta Juma’a kamar yadda aka saba ganin fadakarwa ko nasiha da sauransu ta wannan kafa daga mamallakin katafaren wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

A wannan rana ma dai Alhaji Mustapha A Sani (Mustpha Afuwa) ya sake yin kira da tunatarwa da nasiha.

Saidai yau nasihar ta fada kan mata musamman matan da suke zaune a gidan aure.

“Aure yana da matukar daraja kuma Allah ya sanya albarka a cikinsa, haka zalika aure ibada ne. Ina kira ga mata ku dage da yiwa mazajenku biyayya domin aljannarku tana karkashin kafarsu. Manzon Allah S.A.W yace dukkanin wadda ta kasance tana mai yiwa mijinta biyayya kuma har ta mutu a kan hakan, to aljanna ce makomarta”.

Haka zalika Mustapha A Sani ya yi kira ga maza su kasance masu adalci da kyautatawa iyalansu.

Daga ƙarshe yayi addu’ar “Allah Allah Ka bamu albarkacin wannan rana ta Juma’a Ka kawo zaman lafiya a ƙasarmu ta Najeriya”.

Send:

Leave a Reply