Contact Info

Nasihar Yau Juma’a Daga Bakin Mamallakin Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Alh. Mustapha A Sani.

Kamar yadda kowanne mako mamallakin katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya saba aika saƙo ga al’ummar Misulmi.

A wannan rana ma dai ya sake aika saƙon musamman yadda Azumin watan Ramadan ya ke ƙaratowa.

Aljaji Mustapha A Sani ya bayyana cewar “Tabbas wata mai alfarma ya na gaf da shigowa wato wagan Azumin Ramadan, mu dage da ibada a cikin wannan watan sabo da garabasar da take cikinsa”.

” Wannan watan na Ramadan dai wata ne da babu wani wata kwatankwacinsa kuma tannas wata ne da ake ninka lada a cikinsa, sabo da haka mu dage da ibada a cikinsa mu hana idonmu bacci”.

Daga ƙarshe Alhaji Mustapha A Sani bayyana cewar Allah ya sa zamu shiga cikin watan Ramadan a sa’a kuma yasa muna daga cikin ‘yantattun bayi.

Send:

Leave a Reply