Contact Info

Muna Gudanar da Ayyukan Fitila Mai Aiki da Hasken Rana da Mahadin Fitilar Wato Sollar Daga Kamfaninmu na Afuwa Welding Works.

Katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yana gudanar da ayyuka na fitilu masu aiki da hasken rana dama su kansu mahadin fitilar.

Munsha gayamuku cewar wannan kamfani yana gudanar da ayyuka kala-kala kamar yadda masu bibiyar shafin yanar gizo na wannan kamfani suke gani.

Wadannan ayyukan ma da kuke gani an gudanar dasu a wannan kamfani na sarrafa karfe dake Arewacin Najeriya.

Dukkanin inda wannan katafaren kamfani yaje ya gudanar da ayyukansa to ayyukane masu inganci da nagarta kamar yadda ake samun yabo daga bakin wadanda ake yiwa ayyukan.

Bugu da kari wannan kamfani yana kara bijiro da wasu kalar ayyukan na tafiya dai-dai da zamani cikin sabon salon fasahar zamani.

Dukkanin mai son ganin abubuwan mamaki zai iya zuwa wannan kamfani dake jihar Kano a unguwar Kofar Ruwa Gabas layin Saminu mai siminti domin ganin ayyuka tamkar a kasar China.

Send:

Leave a Reply