Contact Info

Manyan Dalilan da Suka Sanya Kamfanin Afuwa Welding Works Yakawo Injinan Sarrafa Ƙarfe Daga China.

Biyo bayan yadda aketa samun ci gaba da fito da fasaha kala-kala a duniya ta fannoni da dama musamman wajen yin ƙere-ƙere a duniya.

Najeriya dai na daga cikin ƙasashen da suke a nahiyar Afrika kuma ƙasa ce mai tarin al’umma da suka kai sama da Miliyan 230. Yadda bincike ya nuna ana ganin daga yanzu zuwa shekarar 2030 mutanen Najeriya ka iya kaiwa Miliyan 250.

 

Shahararren Kamfanin Sarrafa Ƙarfe mai suna Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance a Najeriya kuma a Arewacin ƙasar wato a jihar Kano a kasuwar Ƙofar Ruwa.

An tattauna da Shugaban wannan kamfani a kafafan yaɗa labarai na Talabijin da Rediyo akan menene ya sa ya kawo manyan injina daga ƙasar China zuwa kamfaninsa na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Alhaji Mustpha A Sani ya bayar da amsoshi kamar haka:

“Ni dai a matsayina na mamallakin wannan kamfani, na duba naga cewar dukkanin Arewacin ƙasar nan tamu ta Najeriya babu wasu manyan injinan da zasu yi kowanne aiki da ake da buƙata musamman wajen sarrafa ƙarfe da kuma lanƙwasa shi, domin wani lokacin saidai ka sayi ƙarfen a Kudancin ƙasar nan a lanƙwasamaka shi sanann a kawo shi Arewacin Najeriya. To hakance ta sanya na kawo injinan zuwa Kano kunga ba sai muntura da ƙarafuna zuwa Kudancin ƙasar nan ba”.

“Sannan kuma dalili na biyu na kawo injinannan daga China ba don komai ba sai don sabo da abokanan sana’a ta, wato idan mutum yanason wani aiki zai iya zuwa muyimasa shi kaga ansamu sauƙi ba sai sunje Kudancin ƙasar nan ba, wannan manyan dalilan sune suka sanya na kawo injinannan”.

Send:

Leave a Reply