Contact Info

Manajan Daraktan Hukumar Dake Kula da Zirga Zirgar Ababan Hawa KAROTA Wato Faisal Mahmud Kabir Ya Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works.

Manajan Daraktan Hukumar Dake Kula da Zirga Zirgar Ababan Hawa KAROTA Wato Faisal Mahmud Kabir Ya Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works.

 

A karshen makonnan wato jiya Asabar Manajan Daraktan hikumar dake kula da zirga zirgar ababan hawa KAROTA ya ziyarci katafaren kamfanin sarrafa karfe da babu kamarsa a Arewacin Najeriya wato Afuwa Welding Works.

Engineer Faisal Mahmud Kabeer ya samu zama gami da tattwunawa da shugaban kamfanin wato Eng. Mustapha A Sani.

Yayin ziyarar sa kamfanin sun zagaya tare da shugaban kamfanin zuwa wajen manya manyan injinan sarrafa karfe a ko wanne sashe na kamfanin domin ganin yadda suke gudanar da ayyukan.

A yayin ziyarar MD na KAROTA Eng. Faisal ya jinjinawa Emg. Mustapha A Sani bisa gagarumin ci gaba da ya kawo a jihar Kano da Najeriya dama Afrika baki daya wajen zamanantar da sana’ar gami da yinta cikin sabon salon fasahar zamani.

Daga karshe ya yi adduar Allah ci gaba da daukaka wannan kamfani da sanyamasa albarka ganin yadda kusan zallar matasa ne suke ayyuka.

Wannan kamfani dai na nan a unguwar Kofar Ruwa Layin Saminu Adamu mai siminti.

Send:

Leave a Reply