Contact Info

Makarantar Alhikma Best Universal Model School Suka Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Gami da Bashi Kyuata ta Musamman.

Yadda Makarantar Alhikma Best Universal Model School Suka Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Gami da Bashi Kyuata ta Musamman. 

 

A ranar Litinin 4 ga watan Maris din shekarar 2024 makarantar Alhikima Best Universal Model School su ka kaiwa shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ziyara wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

Ziyarar dai ta kunshi malaman wannan makaranta gami da wasu daga cikin dalibai maza da mata a safiyar ranar Litinin.

A ziyarar da suka kai ita kanta wannan makaranta ta kaiwa shugaban wannan kamfani kyautar dankareren agogo da aka kera shi domin wannan kamfani.

Lokacin da suka kai wannan ziyara Eng. Mustapha Abdullahi Sani wato shugaban kamfanin na Afuwa Welding Works ya yi jawabai na karawa dalibai gwiwa a kan karatunsu da kuma yimusu alkawarin bayar da gudun mawa idan wasu abubuwan sun taso na taimako.

Engineer Mustapha Abdullahi Sani dai ya saba yiwa makarantu abubuwan alkhairi domin dabbaka adinin Allah.

Ita kanta wannan makaranta ta kasance ana gudanar da karatun addini da kuma na zamani.

A cikin wannan sabuwar shekarar ta 2024 ne wannan makaranta ta Alhikima Best Universal Model School ta gayyaci Engineer Mustapha Abdullahi Sani zuwa wajen saukar karatu da daliban su kayi yayin da ya samu damar halartar saukar.

Wannan makaranta dai ta na nan a jihar Kano a titin Jajira, kuma makaranta ce da ake koyar da karatu cikin nutsuwa da fahimta.

Send:

Leave a Reply