Contact Info

Ma’aikayan Kamfanin Afuwa Welding Works Sun Koma Aiki Ayau Litinin Bayan Kammala Hutun Sallah.

A wannan rana ta Litinin kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works zai dawo aiki biyo bayan hutun sallah da kamfanin ya tafi har na tsawon wasu kwanaki.

Ma’aikatan wannan kamfani mai albarka dai sun kwashe kwanaki 5 suna hutun bikin babbar sallah.

Kuma shi wannan hutu kamar yadda aka saba a duk shekara kamfanin yana bayar dashi kamar yadda kowacce ma’aikata take bayarwa.

A don haka wannan kamfani yake sanarwa da kwastomominsa cewa a wannan rana ta Litinin kamfanin ya dawo aiki kamar ko yaushe.

A madadin shugaban kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Eng. Mustapha A Sani ke yiwa ma’aikatan wannan kamfani barka da dawowa aiki tare da fatan an kammala hutun babbar sallah lafiya gami da kwastomomin wannan kamfani.

Wannan kamfani zaici gaba da farantawa kwastomominsa kamar yadda ya saba wajen yimusu ayyuka masu nagarta da inganci.

Send:

Leave a Reply