Contact Info

Ma’aikatan Kamfanin Sarrafa Karfe na Afuwa Welding Works Sun Kasance Jajirtattu Akan Aikinsu Kamar Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Horas Dasu Akowanne Fanni.

Daga Amina Abdurrahman.

Akwai ma’aikatan kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction daban daban a kowanne sashe.

Kuma ma’aikatan sun kasance na cikin kamfani da kuma wadanda suke a wajen kamfani wato masu aiki a sassan jihoshin Najeriya.

Kowanne a kan aikinsa ya kasance jajirtacce kamar yadda kuke ganin bidiyon ma’aikatan idan suna gudanar da aikiansu.

Ba komai ne ya janyo haka ba sai don irin yadda shugaban wannan kamfani wato Eng. Mustapha A Sani yake tsayawa tsayin daka wajen koyawa ma’aikatansa aiki ba tare da ha’inci ko kasala ba.

Akan hango Engineer Mustapha A Sani a cikin ma’aikatansa sanye da kayan aiki suna gudanar da aiki tare tamkar shima ma’aikacinne, wannan abu yana karawa ma’aikatansa kwarin gwiwa da iya aiki ta wajen idan sunyi kuskure kai tsaye yake nunamusu kuskurensu kuma ya gyaramusu yace ga yadda za su yi.

Haka zalika ma’aikatansa sun kasance akwai manya (seniors) akwai kanana (juniors) kuma akan koyawa mutum aiki daga mataki zuwa mataki domin su sami kwarewa.

Sannan kuma dukkanin irin aikin da za a gudanar Engineer Mustapha A Sani ya san irin ma’aikatan da zai tura domin gudanar da aikin kamar yadda akeson gudanar da aikin na musamman mai nagarta da inganci.

Send:

Leave a Reply