Contact Info

Lambar Yabo: Gamayyar Kungiyar Daliban Najeriya Reshen Jihar Kano Ta Karrama Shugaban Kamfanin Sarrafa Karfe na Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani.

Gamayyar kungiyar daliban kasar Najeriya reshen jihar Kano sun karrama shuganan kamfanin sarrafa karfen na Arewacin kasar da yayi fice wajen sarrafa karfe wato kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Ba komai ne yasa wannan kungiya ta karrama Alhaji Mustapha A Sani ba face yadda yake ci gaba da kawo sauyi mai matukar muhimmanci a fadin kasar nan ta Najeriya.

Haka zalika kungiyar daliban ta bayyana cewar sadaukarwa da jajircewa da aiki tukuru da cikin salo mai kayatarwa na zaburar da matasa da kuma inganta kasar Najeriya musamman bangaren Arewacin kasar wajen kafa wannan kamfani shine babban makasudun da ya sanya suka baiwa Alhaji Mustapha A Sani wannan lambar yabo ta musamman.

Mustapha Afuwa dai naci gaba da karbar lambobin yabo da girmamawa daga bangarori daban-daban na kasar nan wanda ko a iya wannan shekarar ta 2022 ya sami karbar lambobin yabo da yawa.

Shima a nasa bangaren Alhaji Mustapha A Sani ya nuna farin cikinsa dangane da wannan lambar yabo da ya samu daga wannan kungiya ta dalibai ta kasa reshen jihar Kano.

Dukkanin mai son ganin ayyuka na wannan kamfani a rubuce ko a kallo kai tsaye wato bidiyo da hotuna zai iya bibiyarmu a:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter:Afuwa Welding Works.

Gmail:mistyabdul63@gmail.cim

Sannan ga lambobin wayoyinmu can a saman farkon shafin wannan kamfani na yanar gizo.

Send:

Leave a Reply