Contact Info

Kungiyar ASP Ta Baiwa Eng. Mustapha A Sani Lambar Yabo Mai Taken Ambsadan Zaman Lafiya.

Kungiayr Gamayyar Dalibai Ta Zaman Lafiya ta baiwa Eng. Mustapha Abdullahi Sani lambar yabo ta musamman.

Ta bashi wannan lambar yabo ne a yammacin jiya Juma’a a katafaren kamfaninsa na Afuwa Welding Works And General Metal Construction dake unguwar Kofar Ruwa a jihar Kano.

Wannan kungiya wato Association Of Students Peace Ambassadors ta bayyana Eng. Mustapha Abdullahi Sani a matsayin ‘Ambasadan Zaman Lafiya’.

Musamman ta yadda ya kawo ci gaban matasa a Arewa wajen koyamusu sana’o’i domin matukar matashi yana da sana’a to tabbas za a samu zaman lafiya babu su babu taba kayan da ba nasu ba.

A wannan kasar ko a wannan duniyar matukar mutum yana da sana’ar yi to tabbas abin alfahari ne.

Daga karshe Eng. Mustapha A Sani ya yabawa wannan kungiya bisa wannan lambar yabo da suka bashi.

Send:

Leave a Reply