Contact Info

Kungiyar Arewa Students Forum ta Karrama Mustspha A Sani Director General na Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction

Itama kungiyar Arewa Students Forum tabi sahu wajen karrama Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) wato mamallakin katafaren kamfanin sarrafa karfe da ake kira da Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Idan za a iya tunawa a makonni 2 da su ka gabata itama kungiyar Northern Peace Foundation ta karrama Alhaji Mustapha A Sani sakamakon bibiyar ayyukan da kamfanin nasa ya keyi ta kafar sada zumunta da kuma yadda yake baiwa matasa ayyukan yi domin tsamosu daga zaman banza musamman yadda ake da matsaloli a Arewacin Najeriya na rashin ingataccen ilimi ga wasu matasan.

Itama wannan kungiyar wato Arewa Students Forum ta bashi wannan lambar yabo ne badaon komai ba sai yadda ta kirashi mai kishin Arewacin Najeriya da ganin Arewa ta ci gaba musamman ta fannin kere-kere da kuma fito da salo na musamman.

Haka zalika wannan kungiyar Arewa Students Forum ta sake bayyana cewar ta karrama Mustapha A Sani ne biyo bayan yadda yake bayar da ilimi na musamman ga matasa da zarar ya daukesu aiki wato ilimin kere-kere da kirkire-kirkire.

A yanzu dai za a ga dukkanin kasashen da su ka ci gaba za a ga akwai salon fasaha (Technology) da kuma kirkire-kirkire (Creativity). Misali kasar China, yanzu ta kai ta kawo dukkanin inda ka kewaya a duniya sai kaga kayayyakin kasar China ana amfani dasu.

Wannan katafaren kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ta kai ta kawo kowanne irin aikin lankwasa karfe ne to zaiyimaka shi cikin gaggawa sakamakon manyan injinan da ake da su a kamfanin da babu irinsu a Arewacin Najeriya.

Zaku iya bibiyarmu a shafukan sada zumunta kamar haka:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works.

Gmail: mustyabdul63@gmai.com

Adreshi: Kofar Ruwa tsallaken Gabas layin Saminu mai siminti, Kano.

Lambar waya: 08028263771

Send:

116 Comments