Contact Info

Kungiayr Daliban Muryar Arewa Ta Baiwa Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Lambar Yabo Wato Eng. Mustapha Abdullahi Sani.

Kungiyar Daliban Muryar Arewa (VONNIS) ta karrama shuganan kamfanin sarrafa karfe na Arewacin Najeriya Eng. Mustapha Abdullahi Sani.

Ta bashi wannan lambar yabo ne a karshen makon da ya gabata a babbar ma’aikatarsa dake ungiwar Kofar Ruwa a jihar Kano.

Yayin bikin karramawar wannan Kumgiyar Daliban ta yiwa Alhaji Mustapha tambayoyi inda ya yimusu bayani da bakinsa kuma suka karu musamman wajen neman ilimin yadda ake sarrafa karfe.

Daliban sun kwashe fiye da mintina 30 suna yiwa Alhaji Mustapha tambaya kuma kowacce tambaya sukai ya basu amsa dai-dai gwargwado.

Wannan lambar yabo dai sun bayyana cewar sun bashi ita ne badon komai ba sai domin yadda yake bayar da gudun mawar ci gaban al’umma a kasar nan da gina magasa.

Daga karshe Kunhiyar Daliban ta yiwa Alhaji Mustapha Abdullahi Sani godiya da jinjina da yabo bisa lokaci da ya basu na wannan bayar da lambar yabo

Send:

Leave a Reply