Contact Info

Ko Meyasanya Al’umma Suke ci Gaba da Yin Mamaki Dangane da Ayyukan da Suke Gani Daga Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction?

Haryanzu al’umma da dama naci gaba da yin mamaki dangane da wasu ayyukan da suke gani na katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works & General Metal Construction biyo bayan ayyukan kamfanin tamkar a kasar China.

Musamman al’ummar da suke bibiyar shafukan sada zumunta da internet na wannan katafaren kamfani daga jihohi daban-daban.

Hakan na zuwa ne bayan da wannan kamfani yake ta zuwa da sabon salo na ayyuka kala-kala kuma ayyuka tamkar a kasar China da sauran sassan kasashe.

Sai dai Director General na wannan katafaren kamfani Alhaji Mustapha A Sani ya sha fadar wata magana akan ayyukan da kamfaninsa yake gabatarwa.

Ga maganganun da yake fada kamar haka:

“Ni Alhaji Mustapha A Sani ina sake nanatawa mutane cewar dukkanin ayyukan da mutane sukaga mun sanya a shafinmu na sada zumunta na facebook ko a internet wato www.afuwaweldingworks.com ko a shafinmu na twitter Afuwa Welding Works ko kuma wani aiki da mutane suka gani da idonsu a kamfaninmu ko kuma wasu ayyukan da wasu suka gani a wasu jihoshin to babu makawa kamfaninmu ne ya gudanar da aikin, domin mu ba irin wasu kamfanonuwan bane da zamu dauki hoton wani aikin da ba mune muka gudanar da shi ba mu saka shi”.

Haka zalika idan za’a iya tunawa Alhaji Mustapha A Sani idan ana hira dashi a gidan talabijin ko gidajen radio da sauran gidajen jaridu, ya sha fadar cewa kowanne aiki aka gani sun saka hotonsa babu makawa kuma babu shakku kamfaninsa ne ya gudanar da aikin.

Kuma wannan kamfani yana yiwa al’umma albishir da cewa tabbas ako da yaushe suna kan kirkirar ayyuka na musamman kuma masu sabon salo da ba a fiye ganin irinsu ba kuma masu nagarta.

Zaku iya bibiyarmu a shafuka kamar haka:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works.

Gmail:Mustyabdul63@gmail.com

Send:

Leave a Reply