Contact Info

Ko Kun San Dalilan Dayasa Ma’aikatanmu Suka Kware Kan Aiki a Fannoni Daban Daban a Kamfanin Afuwa Welding Works?

Kamar yadda mabiya shafukanmu a kasashe da dama da sauran sassan duniya suke mahanar cewar ma’aikatan kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works kowa kwararre ne wajen aiki.

Saidai wasu suna tambayar cewa shin akwai wata makaranta da suke shiga ne ta koyon aiki da malamai suka horas dasu kafin akawosu kamfanin?

Magana ta gaskiya babu wata makaranta da su ka shiga, saidai kamfanin na Afuwa Welding Works ya kasance tamkar makaranta biyo bayan yadda shi shugaban wannan kamfani ya zamanto malami a fannin koyawa ma’aikatansa aiki.

Domin kamar yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sha fadar cewa kamfaninsa tamkar makaranta ne biyo bayan ya kan koyawa ma’aikata matakan aiki daki daki.

Kamar yadda ake ganin yadda wadannan ma’aikatan suke gudanar da aikin walda cikin kwarewa da basira gasuman sunyi reras kowa yana aikinsa na hada fitilun kan titi.

Daga karshe babbar amsarmu ga masu bibiyarmu itace kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction makaranta ce ta musamman.

Send:

Leave a Reply