Contact Info

Kasar China: Bayanai Gami da Hoton Zuwan da Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Yayi Zuwa Kasar China Wato Eng. Mustapha A Sani a Wasu Shekaru da Suka Shude.

A wannan shafi namu na dandalin sada zumunta an ga hotuna gami da bidiyo dangane da ziyarce ziyarcen da Eng. Mustapha A Sani ya je kasar China.

Kuma a cikin hotunan an ganshi a gurare masu yawa a kasar ta China wato yaje gurare da dama akan huldar kasuwancinsa

Wannan hoton ma da kuke gani a wajen wani cin abinci ne lokacin da ya ziyarci kasar China a shekarun baya.

Kasar China dai ta kasance a ma’aikatu da yawa ba a iya bambance mata da maza idan suna gudanar da aiki matukar mutum ba zuba ido yayi ba sosai, domin yadda maza suke kera mashina da injina haka suma matan sukeyi.

Kuma al’adarsu ce matukar mutum yaje yin siyayya a wani kamfani sukan zagaya dashi su girmama kwastoma a kaika inda kake so.

Send:

Leave a Reply