Contact Info

Karamar Hukumar Babura: Ayyukan da Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya Gudanar a Babura Dake Jihar Jigawa.

Tabbas Hausawa na cewa sayen na gari mai da kudi gida, kamar yadda katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya saba lekawa lunguna da sakuna a sassa danan-daban na kasar nan ta Najeriya.

Wannan kamfani dai ya zamanto hantsi leka gidan kowa domin kuwa kowacce jiha a Najeriya akwai ayyukan wannan kamfani.

A wannan lokacin dai mun sake komawa jihar Jigawa inda a shekarun baya wannan kamfani ya gudanar da wasu ayyuka na kwantainoni da sauran wasu ayyukan da su ka danganci karfe.

Wannan Karamar Hukumar maisuna Babura ta kasance a jihar Jigawa wato jihar nan da ta ke a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ita dai wannan Karamar Hukumar ta Babura ta kasance a Arewacin jihar Jigawa, haka zalika Babura ta yi iyaka da Karamar Hukumar Baure ta jihar Katsina daga bangaren Arewa, sannan kuma tayi iyaka da Karamar Hukumar Kazaure daga Yamma.

Idan aka yi duba za a ga tayi iyaka da Karamar Hukumar Sule Tankarkar daga Gabas, sannan kuma tayi iyaka da Karamar Hukumar Dambatta daga Kudancin wannan Karamar Hukuma.

A wannan Karamar Hukumar ta Babura kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya zubar da basirarsa wajen yin ayyuka masu nagarta da inganci.

Kuma ayyukan da kamfanin ya gudanar har yanzu suna nan tamkar sababbin ayyuka kan yadda suke da nagarta.

Domin ganin ayyukan da muke gudanarwa da kuma wadanda muka gudanar a shekarun baya, zaku iya bibiyarmu a:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works.

Send:

Leave a Reply