Contact Info

Kannywood: Muna Jin Dadin Ziyartar Kamfanin Afuwa Welding Works Domin Gudanar da Yin Fina-Finai.

Wasu daga cikin ma’aikatan masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood sun bayyana jin dadinsu idan suna ziyartar katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction domin yin fina-finansu.

Idan za a iya tunawa ko da a cikin wannan shafi na wannan katafaren kamfani za a dinga ganin hotunan wasu ‘yan Kannywood da kayan aikin wannan kamfani a lokacin da suka ziyarci kamfanin domin yin daukan film dinsu wato (Shooting).

Wasu daga cikin ‘yan fim din da suka taba ziyartar wannan kamfani domin gudanar da fina-finasu akwai Yahaya S. Fulani da Isah Peroskhan (Presidor) da Maimuna da sauransu.

Haka zalika a masana’antar ta Kannywood shima shahararren mawakinnan wato Aminu Ala (Alan Waka) ya taba ziyartar wannan kamfani kuma ya shiga lunguna da sakuna, sannan shi kansa ya yaba da abin musamman yadda aka kera wannan kamfani tamkar a kasar China.

Masana’antar ta Kannywood dai tana nuna jin dadinya wajen ziyartar wannan kamfani badon komai ba sai don yadda shine kamfanin da yafi keruwa yafi haduwa sannan kuma ga kayan aiki tamkar kana kasar China.

“Tabbas kamar yadda muke ziyartar wannan kamfani na Alhaji Mustapha A Sani muna gudanar da fina-finanmu, to zamuci gaba da yi musamman ma yadda shi kansa Mustapha A Sani yake yin maraba damu idan munje kuma da yadda yake sakarmana fuska” acewar ma’aikatan Kannywood.

Send:

Leave a Reply