Contact Info

Kamfanin Sarrafa Karfe na Afuwa Welding Works Naci Gaba Kawata Kasar Nan Ta Fannonin Kirkirar Abubuwa na Musamman.

Katafaren kamfanin sarrafa karfe na Arewacin kasar Najeriya kuma mallakin fasihin gwani a fannin kirkira Engineer Mustapha Abdullahi Sani naci gaba da kawata kasar nan wajen yin ayyuka da kirkire-kirkire.

Hakan ya biyo baya ne kan yadda kowanne sashe na wannan kamfani akan tunanin kirkirar abubuwa suke kuma cikin sabon salon fasahar zamani.

A kowanne mako ko wata dukkanin mabiya manyan shafukan sada zumunta na wannan kamfani sai sunga sabon abu ko wata sabuwar kirkira da Eng. Mustapha A Sani ya fitar kuma ta zamo dai-dai da zamani.

A tattaunawar shafin yanar gizo na wannan kamfani da Eng. Mustapha Abdullahi Sani wato www.afuwaweldingworks.com ya bayyanamana cewar shifa ko yaushe a cikin bincike yake wajen kawo abin da babu irinsa ko kuma yadda zai kirkiri abubuwa na musamman da babu irinsu domin zamanantar da kamfaninsa.

Ya kara da cewar a yanzu haka dukkanin wanda ya ziyarci kamfaninsa zata zaiyi kamar a kasar China yake idan yaga yadda ake yiwa karfe wato sarrafa shi.

Daga karshe Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya karkare da cewar nan gaba za’ai ta ganin sabuwar kirkirarriyar fasaha akan ayyuka da dama a wannan kamfani.

Send:

Leave a Reply