Contact Info

Kamfanin Afuwa Welding Works Yayi Jinjina ga Kwastomominsa da Mabiyansa na Yanar Gizo da Kuma na Dandalin Sada Zumunta Wato Facebook da Twitter da Sauransu.

Katafaren kamfanin sarrafa karfe a fadin tarayyar kasar nan wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction yayi jinjina ga mabiyansa da kuma kwastominsa.

Mabiyan nasa dai sun kasance na kan yanar gizo (Internet)wato masu bibiyar www.afuwaweldingworks.com daban-daban a fadin duniya, da sauran mabiyansa na dandalin sada zumunta kamar shafin facebook da kuma twitter.

Wannan jinjina da godiya sun biyo bayane ta wajen yadda al’umma daga kasahe daban-daban suke karanta labaran wannan kamfani na kan yanar gizo (Internet) da masu bibiyar shafin faceboo a kasashe daban-daban da kuma shafin twitter na wannan kamfani.

Haka zalika wannan kamfani yana jinjina da godiya dangane da yadda sababbin al’umma suke karuwa a kullum wajen bibiyar wannan kamfani da masu yin ta’aliki (comments) a shafukan facebook da twitter da kuma ta cikin yanar gizo.

Wannan kamfani kuma yayi godiya da jinjinar ban girma ga kwastomominsa na kusa da kuma na nesa wato sauran sassan jihoshin kasar nan da suke yabawa kamfanin wajen ayyuka masu nagarta.

Daga karshe Darakta Janaral na wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani ya bayyana cewar bashi da buri illa ci gaba da raya yankin Arewacin kasar nan ta Najeriya ta fannin sarrafa karfe da kuma ci gaba da yiwa kwastomomi ayyuka masu nagarta.

Sannan kuma yana godiya ga mabiya shafukan sada zumunta na wannan kamfani dangane da irin addu’o’in da sukeyimasa ta yadda ya kawo gagarumin ci gaba a Arewacin Najeriya.

Send:

Leave a Reply