Contact Info

Kamfanin Afuwa Welding Works ya Gabatarwa da Mai Martaba Sarkin Kano Hotonsa da Akazanamasa a Jikin Karfe Wato Alhaji Aminu Ado Bayero C.F.R.J.P a Fadarsa.

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gabatarwa da mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero katafaren hotonsa da aka zanamasa.

An gabatarmasa dashi ne a a jiya Alhamis a fadarsa dake cikin kwaryar birnin Kano wato fadar da take da cikakken tarihi kenan.

Wannan kamfani dai ya kafa gagarumin tarihi wanda a karon farko shine kamfanin da ya fara fitar da zanen mai martaba sarkin Kano a jikin karfe.

A nasa bangaren sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi jawabin godiya dangane da wannan aikin da kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya yi na zana hotonsa.

“A madadina da masarautata ta Kano, muna godiya ga wannan kamfani mai albarka da shi kansa shugaban kamfanin Afuwa Welding Works wato Eng. Mustapha A Sani da wannan gudun mawa, muna godiya sosai kuma muna alfahari da wannan kamfanin a jiharmu ta Kano da Najeriya dama duniya baki daya”.

Shima a nasa bangaren shugaban kamfanin Afuwa Welding Works Eng. Mustapha A Sani ya nuna jin dadinsa dangane da tarihin da kamfanin sa na Afuwa Welding Works ya kafa wajen zana wannan hoto a masarautar ta Kano.

Wannan kamfani dai naci gaba da fito da martabar Kano da Najeriya a idon duniya biyo bayan yadda yake gudanar da kere-kere tamkar a kasar China.

Send:

Leave a Reply