Contact Info

Kamfanin Afuwa Welding Works Ya Fitar Da Rangadeden Zanen NDLEA Wato Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ajikin Karfe.

Kamar yadda kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake gudanar da aikin zane ko wanne iri ne kamar yadda ake gani ako da yaushe.

Yanzu ma gashi kamfanin ya fitar da zanen aiki a jikin karfe na Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).

Wannan alamar zane dai ya kasance na karfe kuma inganacce kamar yadda ake ganinsa a haka tun kafin ayimasa fyanti.

Idan za a iya tunawa wannan kamfani a kullum sai ya fitar da sabon zane da babu irinsa ciki harda zanen hotunan mutane da sauransu.

Wannan kamfani zaici gaba da zuwarmuku da sabon salo ako da yaushe, kuci gaba da bibiyar shafukan sada zumunta na kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works domin ganin ayyukanmu sababbi ako da yaushe.

Send:

Leave a Reply