Contact Info

Kamfanin Afuwa Welding Works Naci Gaba da Mamaye Najeriya da Afrika Dama Duniya Baki Daya Biyo Bayan…

Kamfanin Afuwa Welding Works Naci Gaba da Mamaye Najeriya da Afrika Dama Duniya Baki Daya Biyo Bayan…

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction naci gaba da mamaye jihar Kano da Najeriya da Afrika do duniya baki daya.

Hakan ya biyo baya ne sakamakon yadda kamfanin yake ci gaba da bijiro da ayyuka kala kala da kuma inganta ayyukan musamman wajen (finishing) gami da sabon salon fasahar zamani.

Yanzu wannan kamfani naci gaba da bunkasa kan yadda ake kara saninsa a duniya baki daya musamnan ta hanyar yanar gizo (Internet) da kuma sauran shafukan sada zumunta da suka hadar da facebook da Instagram da Threads da Twitter da sauransu.

Akwai al’umma da dama daga sassan nahiyoyin duniya da suke ci gaba da turo sakonni akan yadda Allah Ya azurta Najeriya da wannan katafaren kamfanin sarrafa karfe da ake alahari dashi kuma ake kawo ayyuka daga kasashen waje.

Mutanen kasar China sun kasance suna kawo ziyara wannan katafaren kamfani kuma da zarar sunzo abin mamaki yake basu domin dauka suke tamkar a kasarsu ta China suke.

Shi kansa shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Engineer Mustapha A Sani ya ziyarci kasar China sau da yawa a kan huldar kasuwancinsa.

 

 

Haka zalika har yanzu yakan ziyarci kasar ta China domin ci gaba da fadada kamfaninsa ta fannin kirkira da ayyukan salon fasahar zamani.

Send:

Leave a Reply