Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction na yin kofofin zamani masu inganci da nagarta gami da tafiya dai-dai da zamani.
Kofofin sun kasance kala-kala kama daga kananun kofofi har manya wato gates a turance, sannan uwa uba kuma har da kofofin gidan sarauta wannan kamfani yana yin su.
Matukar mutum yanason ayimasa kofofi masu inganci da nagarta wato mahadi ka ture to babu makawa ya tawo kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.
Wannan kamfani ya kware wajen sarrafa karfe ko wanne iri ne domin yimasa ado da kwalliya gami da kawata shi.
Wannan kamfani yana maraba da kwastomin sa daga sassan kasashen duniya kamar yadda suke yawan ziyartar wannan kamfani ako da yaushe.




