Contact Info

Kalli Bidiyo da Hotuna Gami da Jawaban Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works ya Zana Hoton Alh. Atiku Abubakar Ajikin Karfe Cikin Salo da Fasaha.

 

Kamar yadda aka sani kamfanin Afuwa Welding Works ako yaushe a kan kirkira ya ke kuma ake kirkirar sababbin abubuwa.

Kamar yadda ake gani wannan bidiyon lokacin da katafaren injin CNC Plasma Cutting Machine ne ya kammalla zanen hoton dan takarar shugaban kasa na Najeria a karkashin inuwar jam’iyyar PDP mai alamar lema.

Kamfanin ya yi amfani da sabon salon fasahar zamani domin zana hotonsa a jikin karfe gami da rubututtuka a jiki.

Daya daga cikin hotunan da kuke gani dai lokacin da aka kammala aikinne ba tare da anyimasa fenti ba.

Haka zalika sauran hotunan kuma da kuke gani lokacin da aka kammala yiwa hoton fenti ne wato lokacin da komai ya kammala.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2022 da ta gabata wannan kamfani na Afuwa Welding Works ya yi ayyuka na ban mamaki kuma kala-kala wanda daga ciki har da dawisu (peacock) da wani hoton masarauta.

Haka zalika wannan hoto an yishi ne domin sanya shi a jihar Kano kamar yadda ake ganin rubutun Kano a jikin wannan hoto.

A ranar 9 ga watan Feburairu Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci Kano kuma wannan zanen hoton anyishi ne sakamakon wannan zuwa nasa.

Idan zaku iya tunawa an hango shugaban wannan kamfani Engineer Mustapha A Sani yana cewa tabbas a wannan shekarar wannan kamfani yazo da salo na musamman domin dorawa daga inda ya tsaya.

Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance kamfanin da ake alfahari dashi a kasar Kano da Najeriya dama nahiyar Afrika baki daya.

Send:

Leave a Reply