Contact Info

Kaf Najeriya Babu Kamfani Mai Tafiya da Zamani Kamar Kamfanin Afuwa Welding Works a Fannin Sarrafa Karfe Kamar Yadda Masana Suka Fitar da Alkaluma Bisa Wasu Manyan Dlilai.

Daga Amina Abdurrahman.

Masana a sassa daban daban na duniya naci gaba da tofa albatkacin bakinsu dangane da yadda ake kara zamanantar da kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ta ko wanne fanni.

Kama daga fannin yadda ma’aikatan suke aiki da yadda ake gudanar da aiki mai nagarta ba tare da son zuciya ba.

Masu fitar da alkaluma a sassa daban daban na duniya da nan nahiyar Afrika da kuma gida Najeriya suna bibiyar shafukan sada zumunta na wannan kamfani domin ganin irin ayyukan da ya yi a Kano da sassan jihoshin Najeriya da kuma yadda ake kawowa kamfanin aiki daga wasu kasashen nahiyar Afrika.

Wannan kamfani dai na Afuwa Welding Works ya gudanar da ayyukan raftar karfe da saka fitilunn sola da gina jami’o’i da saka fayif na ruwa a kusan kowacce jiha a Najeriya Kama daga Senate Building na jami’ar Bayero da madatsar ruwa ta Obajana inda Alhaji Aliko Dangote yake yin siminti da kuma can ayyukan saka pipe a Mambila dake jihar Taraba tare da manyan ayyukan tankuna na ruwa.

Haka zalika idan akadawo maganar ayyukan da wannan kamfani yake gudanarwa a cikin kamfanin, akwai injina na zamani da iya wannan kamfani ne kadai yake dasu kamar yadda ake ganin injinan gasunan.

Sannan kuma an tabbatar da cewar kaf kasar Najeriya babu kamfanin sarrafa karfe mai tafiya da zamani a fannin dandalin sada zumunta da shafin yanar gizo (Internet) ta yadda ana kallon ayyukansu a sassan duniya sai kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Bisa wadannan dalilai masana suka suka dinga tura sakonni ta shafin yanar gizo na wannan kamfani, kama daga Turawa da mutanen kasar China da mutanen Latin da mutanen nahiyar Afrika dama wasu daga nan Najeriya.

Daya daga cikin ma’aikatan sashen yanar gizo na wannan kamfani wato Amina Abdurrahman ta kwashe makonni 3 tana tattara alkaluman masanan da suka yabawa wannan kamfani wajen tafiyar da ayyukansu da zamani musamman yadda suke da manyan injinan da babu irinsu a Arewacin Najeriya dama dama Najeriya baki daya.

Musamman yadda masu bibiyar wannan kamfani da kuma shafukansa ganin cewa ansake saka sababbin injina sannan kuma za a sake saka wasu injinan.

Wannan kamfani yana godiya dangane da wannan yabo na alkaluma da masana suka tattara kuma suka tabbatar babu kamfani mai tafiya da zamani kamar kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works.

Send:

Leave a Reply