Contact Info

Juma’a: Yadda Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Yayi Wata Tunatarwa Gami da Fadakarwa Wato Eng. Mustapha A Sani.

A wannan rana ta Juma’a mai albarka kamar yadda ya saba a kowanne mako shugaban wannan kamfani na sarrafa karfe Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya yi fadakarwa gami da tunatarwa ga ‘yan uwa Musulmi.

A bangaren tunatarwa dai ya yi kira ga ‘yan uwa Musulmi da a dage da ambaton Allah da kiyaye dokokinSa.

“Ina sake tunatar da ‘yan uwa Musulmi da mu dage da ambaton Allah da yimasa biyayya, tabbas zamu kara samun nutsuwa da albarkar rayuwa da zama cikin salama”.

Haka zalika a bangaren fadakarwa ma ya yi kira ga iyaye tabbas su kasance suna saka ido a kan ‘ya’yansu da janyo su a jiki domin sanin halin da suke ciki, da kuma bincike a kan da wadanne irin abokai suke ma’amala, domin ‘ya’ya amana ce Allah Ya baiwa iyaye.

Bugu da kari Eng. Mustapha A Sani ya sake yin tuni dangane da wannan duniyar da kuma lahiya

“Ina sake tunatarwa akan cewa kada ka yarda ka salwantar da lahirarka don wannwn duniyar da babu tabbas a cikinta, ita wannan duniyar dangane da lahira kamar ka rufe ido ne ka bude, ga ma wanda rayuwa ta tsawaita”.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya yi adduar Alllah sadamu da alkairan dake cikin wannan rana Ya kiyayemu da dukkanin abin ki dake cikin wannan rana.

Send:

Leave a Reply