Contact Info

Juma’a: Tunatarwa Ta Musamman Awannan Rana Mai Albarka Daga Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Eng. Mustapha A Sani.

Kamar kowanne mako na ranar Juma’a an saba jin tunatarwa ko fadakarwa ko nasiha daga mamallakin kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Alhahi Mustapha A Sani dai ya kasance yana tunatar da al’umma Musulmi dangane da wasu abubuwa musamman na addini ko zamantakewar rayuwa da sauransu.

A wannan rana tunatarwar ta gangaro kan iyaye musamman masu ‘ya’ya da basa bibiyar abubuwan da ‘ya’yansu su ke yi.

“Ina kira ga iyaye musamman wadanda ba sa bibiyar halin da ‘ya’yansu suke ciki, to ya kamata su tashi tsaye su san su waye abokan ‘ya’yansu, da suwa suke mu’amala, sannan kuma su kula da tarbiyyar su domin tun yaro yana karami ya kamata ka dora shi a kan hanya mai kyau”.

Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya kara da cewar wannan zamanin da ake ciki a yanzu tabbas iyaye su kasance masu yiwa ‘ya’yansa addua.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya yiwa al’ummar Musulmi barka da Juma’a, fatan Allah bamu albarkacin wannan rana.

Send:

Leave a Reply