Contact Info

JUMA’A: Tunatarwa Gami da Fadakarwa a Wannan Rana ta Juma’a Daga Eng. Mustapha A Sani Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works.

A wannan rana mai albarka kuma Juma’a ta farko a cikin sabuwar shekarar Musulunci kamar kowanne mako shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works ya saba yiwa ‘yan uwa tunatarwa gami da fadakarwa.

A yau din dai Alhaji Mustapha A Sani ya yimana tunatarwa akan wani hadisi gami da fa’idodin hadisin.

“A matsayina na shugaban wannan kamfani mai albarka ina yiwa Allah godiya da Ya nunamana Juma’a ta farko a wannan sabuwar shekarar ta Musulunci ta 1445 AH. Allah sadamu da alkhairan dake cikinta Ka karemu da sharrin dake cikinta”.

Yau zanyimana tuni dangane da wani hadisi.

Daga Abu Amr, ana kuma ce masa Abu Amrah, Sufyanu ibn Abdullah yardar Allah ta tabbata a gareshi, ya ce:

((Na ce: Ya Manzon Allah! Ka fadamin wani zance da a cikin Musulunci da ba zan tambayi kowa ba shi sai kai. Sai ya ce: “Kace nayi imani da Allah sannan ka tsaya dai-dai (a kan hanyar gaskiya)”)). Muslim ne ya rawaito wannan hadisi.

Fa’idodi Daga Cikin Wanna Hadisi.

1. Fa’ida ta farko a cikin wannan hadisi itace, lallai imani da Allah shine kan gaba kan dukkanin wani aiki na gari.

2. Gamsuwa da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya yiwa dukkanin al’ummar Musulmi fatan alkhairi a wannan rana mai albarka.

Send:

Leave a Reply