Contact Info

Juma’a: Sakon Tunatarwa Gami da Fadakarwa Daga Eng. Mustapha Abdullahi Sani Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works.

Kamar ko wanne mako kuma aka saba tunatar da ‘yan uwa Musulmi dangane da fadakarwa ko tunatarwa a wannan rana mai albarka.

A yau din dai shugaban katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya yi kira da tunatarwa ta musaman.

Yayi wannan tunatarwa ce aka ayyukan alkhairi da ake son aikata shi a ko yaushe.

“Ina tunatarwa da al’umma kuma ‘yan uwa Musulmai akan mu ci gaba da dagewa wajen aikata ayyukan alkhairi, domin ako da yaushe mutum zai iya aikata wa, da karfinsa ko da kudinsa da sauran hanyoyin aikata alkhairi. Tabbas akwai lada acikin yin ayyukan alkhairi”.

Daga karshe Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya taya al’ummar Musulmi barka da wannan rana ta Juma’a.

Sannan ya yi adduar Allah hadamu da alkhairan dake cikin wannan rana kuma Allah kiyaye mu da dukkanin wani abin ki.

Send:

Leave a Reply