Contact Info

JUMA’A: Sakon Barka da Juma’a Daga Eng. Mustapha A Sani Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

A wannan rana ta Juma’a kamar yadda aka saba ako wanne mako ana ganin fadakarwa da tunatarwa ta ranar Juma’a, a rubuce ko a fefen bidiyo ko kuma a saurara.

A wannan rana ma dai shugaban wannan kamfani mai albarka Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya sake yin tunatarwa ga ‘yan uwa Musulmi.

“Ina kira da tunatarwa ga iyaye akan ku kula da tarbiyyar ‘ya’yansu gami da su wanene abokansu, domin ‘ya’ya amana ce Allah Ya bamu, domin wasu iyayen suna sakaci da lamarin ‘ya’yansu ta fannin tarbiyya da kuma saikemusu hakkokinsu”.

Haka zalika Alhaji Mustapha A Sani ya yi kira ga mutane da su kasance masu kyautatawa iyayensu domin basu da kamarsu ta yadda zasu sami albarka.

Daga karshe ya yo adduar Allah sada mu da alkairan dake cikin wannan rana sabanin haka kuma Allah kare mu. Ameen.

Send:

Leave a Reply