Contact Info

Juma’a: Sako Gami da Tunatarwa Awannan Rana Ta Juma’a Kamar Yadda Aka Saba Daga Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Eng. Mustapha A Sani.

Kowanne mako akwai sako ko tunatarwa ko fadakaraa da yake zuwa daga bakin mamallakin katafaren kamfanin sarrafa kafre na Afuwa Welding Works Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

A wannan rana ta Juma’a Alhaji Mustapha A Sani ya yi kira akan a dinga kulawa da marayu.

“Tabbas kulawa da maraya ko marayu wani al’amari ne babba da tabbas sai an dage an jajirce wajen wajen yin wannan aikin lada, domin akwai lada mai train yawa da Allah zai baiwa mutum idan ya tallafawa marayu”.

Alhaji Mustapha A Sani ya kara da cewar yana kira ga al’umma da su zamo masu jin kan marayu.

Daga karshe ya yi addua’ar Allah bamu albarkacin wannan rana ta Jima’a, Ya kiyayemu da dukkanin sharrin dake cikinta Ya hadamu da alkhairan dake cikin wannan ranar.

Send:

Leave a Reply