Contact Info

Juma’a: Kalaman Managing Director na Kamfanun Afuwa Welding Works Awannan Rana Mai Albarka.

Kamar kowanne mako a wannan rana ta Juma’a shugaban wannan katafaren kamfani na sarrafa karfe na Afuwa Welding yakan tunasar da ‘yan uwa Musulmi.

Tunasarwar ta kan zo ta bangarori da dama ko kuma nasiha ko fadakarwa musamman akan addini da zamanyakewar rayuwa akan Musulunci.

A wannan rana Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’umma cewa su yi kokarin zamowa mutanen kirki.

“Mutum ya zamo mutumin kirki a fili da kuma boye, domin tabbas mutumin kirki ako yaushe yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma ako ina ana shaidarsa, sannan mutumin kirki yana rabauta duniya da lahira kuma Allah yana sakashi a Aljanna da RahamarSa”.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani yayi addua’ar Allah kawo zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali ako ina a fadin duniya musamman a kasarmu ta Najeriya.

Send:

Leave a Reply