Contact Info

Juma’a: Alhaji Mustapha A Sani Yayi Kira da Nasiha Akan ‘Yan’uwa Musulmi Awannan Rana ta Juma’a.

Cikin ikon Allah mun shiga Juma’a ta biyu a cikin Azumin watan Ramadan wato wata mai albarka.

Kamar kowanne mako mamallakin katafaren kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya kan faɗakar ko ya yi nasiha da wa’azantarwa.

A yau dai Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’umma da mu zamo masu yin kyakyawan zato ga ‘yan uwanmu, biyo bayan babu kyau a matsayin Musulmi ya dinga yiwa wani mummunan zato.

Daga ƙarshe Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’ummar Musulmi da mu dage da ibada a wannan wata mai alfarma na Ramadan domin samun rabauta a rana gobe Alƙiyama.

Send:

Leave a Reply