Contact Info

Juma a: Sakon Fadakarwa da Tunatarwa Daga Bakin Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Eng. Mustapha Abdullahi Sani.

Yau Juma’a 5 ga watan Safar, 1444. Wanda yayi dai-dai da 2 ga watan Satumba, 2022.

Kamar kowanne mako shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya saba tunatar da ‘yan uwa Musulmi da fadakarwa da kuma wa’azantarwa.

A yau dai Alhaji Mustapha yayi tunatarwa ‘yan uwa abubuwa guda uku (3) da suka hadar da:

1. Ako yaushe mu tuna cewa ba mune muka halicci kanmu ba, Allah ne ya haliccemu.

2. Tunda munyi imanin cewa Allah ne ya halicce mu, sannan munyi imani cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muci gaba da dagewa da bayar da himma wajen yimasa bauta. Idan muka tuna da ayar nan cewa Allah yace, “Ban halicci mutum da aljani ba sai domin su bauta Min”.

3. Mu tuna cewa tabbas zamu koma ga Allah, wato zamu mutu.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya bayyana cewar mu dage da ayyukan alkhairi ako da yaushe.

Send:

Leave a Reply