Contact Info

Jawabai Cikin Hotunan Ayyukan Lankwasar da Karfe Daban Daban a Shafin Yanar Gizo na Afuwa Welding Works

Jawabai Cikin Hotunan Ayyukan Lankwasar da Karfe Daban Daban a Shafin Yanar Gizo na Afuwa Welding Works

 

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction kamfani ne da aka kafa shi domin kere-kere da sarrafa karfe ko wanne iri ne.

Kuma kamfanine kusan tsawon shekaru 40 kenan da kafuwarsa, haka zalika kamfani ne da yake gudanar da ayyuka a sassan jihoshin kasar Najeriya, haka zalika kamfani ne da al’umma daga kasashen waje suke zuwa ake yimusu ayyuka musamman daga Senegal da Niger da Togo da Cameroon da Chad da sauransu.

Wadannan karafuna da ku ke kallo tabbas kafin ayimusu haka a mike suke, kawai anason ayimusu irin wannan lankwasar da kuke gani shine aka yi amfani da kwarewa wajen sarrafa karfe aka lankwasa su.

Haka zalika sauran da kuke ganinsu anyimusu joni suma a kamfanin aka yumusu hakan ta sigogi daban-daban da aka gudanar dasu aka kaisu zuwa wasu sassan jihoshin na Najeriya.

Idan za a iya tunawa shugaban wannan kamfani kuma kwararren Engineer wato Alhaji Mustapha A Sani a wani fefen bidiyo da muka taba sanyawa a wannan shafi ya bayyana cewa karfe kowanne iri ne kuma komai kaurinsa to za a lankwasa shi ayimasa yadda a keso a wannan kamfani.

Wani karfe akan tankwarashi fiye da wadannan, kawai dai ya danganta da irin yadda a keson yiwa karfen.

Bugu da kari wannan aiki da kuke ganinsa wannan kamfani ya kafa tarihin lankwasar da shi a lokacin da wani dan kasar India ya kawo aikin aka yimasa kuma ya tafi dashi zuwa can kasar India.

Kuci gaba da bubiyar shafukan sada zumunta na kamfanin sarrafa karfe da babu tamkarsa a Arewacin Najeriya domin ganin ayyukansu kala-kala wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Send:

Leave a Reply