Contact Info

Goron Juma’a Daga Bakin Darakta Janar na Kamfanin Afuwa Welding Works.

A wannan rana ta Juma’a wato Juma’a babbar rana shugaban kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato kamfanin sarrafa karfe ya mika sakon barka da Juma’a.

A yau dai Alhaji Mustapha Afuwa ya tabo bangaren cewa al’ummar kasar Najeriya a dage da addu’o’i da neman zaman lafiya a wajen Allah S.W.A domin shine kadai zai yayewa al’ummar kasar nan damuwar da take damun kowa.

“Ya kamata mu dage da addu’o’i da kuma duba dukkanin inda mukeyin kura-kurai mu gyara su, idan muka gyara to Allah S.W.A Zai kawomana sauki”

Haka zalika Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya bayyana cewar mu dinga tunawa ako da yaushe Allah zai iya karbar ranmu, ya kamata mu dinga yin alkhairi da bautawa Allah domin mutuwa ko yaushe na iya riskarmu.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani yayi addu’ar Allah ya zaunarmana da kasarmu ta Najeriya lafiya, sukama marasa lafiya Allah basu lafiya.

Send:

Leave a Reply