Contact Info

Goron Barka da Juma’a Daga Darakta Janar na Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

A yau take Juma’a kuma rana mai mafi girma a cikin ranakun da Allah S.W.A ya halitta.

Kamar kowacce rana Darakta Janar na wannan katafaren kamfaniAlhaji Mustapha A Sani ya saba yin nasiha da fadakarwa ga al’ummar Musulmi.

A yau ma Alhaji Mustapha A Sani ya sake yin wannan nasihar ga al’umma dangane da biyayya akan iyaye.

“Ina kara kira ga al’umma musamman yaran wannan zamanin harda ma manyan cewa, biyayya ga iyaye tana da matukar muhimmanci, domin mutum bashi da kamarsu”.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya kammala nasihar da cewa dukkanin mai biyayya ga iyayensa kuma yana farantamusu to zai kasance mai nasara da samun albarka a cikin rayuwa.

Send:

Leave a Reply