Contact Info

Gagarumar Lambar Yabo: Gamayyar Kungiyar Daliban Yammacin Nahiyar Afrika ta Karrama Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mistapha A Sani

A yammacin jiya Lahadi 7 ga watan Ogusta, 2022 shugaban kamfanin sarrafa karfe da babu kamarsa a Arewacin Najeriya wato Alhaji Mustapha A Sani ya samu wata gagarumar lambar yabo.

Wannan lambar yabo da Alhaji Mustapha A Sani ya samu, ya same tane daga gamayyar kungiyar daliban nahiyar Afrika ta Yamma.

Wannan lambar yabo dai lambar yabo ce ta musamman biyo bayan yadda wannan kungiyar ta duba taga ya dace ta karrama Eng. Mustapha A Sani domin irin gagarumar da yake bayarwa.

Wannan kungiya dai ta bayyana cewar yadda ta ga Alhaji Mustapha A Sani yake baiwa matasa ilimi da koyamusu sana’o’i da ciyar da kasar Najeriya gaba ta fannin kere-kere yasa suka karrama shi.

Yayin wannan karramawa wannan kungiyar ta sake jinjina ga Alhaji Mustapha A Sani wajen jajircewarsa a wannan yanki na Arewacin Najeriya.

Daga karshe shima Eng. Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) yayi godiya ga Allah da kuma godiya da wannan kungiya ta daliban Yammacin Nahiyar Afrika wajen wannan lambar yabo da suka bashi.

Send:

Leave a Reply