Contact Info

Ga Sabon Albishir Daga Kamfanin Afuwa Welding Works ga Al’ummar Jihar Kano da Najeriya da Afrika Dama Duniya Baki Daya.

A dai-dai lokacin da shekarar 2022 ta ke gaf da karewa katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya zo muku da sabon albishir.

Wannan sabon albishir dai albishir ne da zai amfani al’ummar jihar Kano da Najeriya da sassan nahiyar Afrika dama duniya baki daya.

Kamar yadda aka sani wannan katafaren kamfani babu tamkarsa a Arewacin kasar Najeriya wajen kayayyakin aiki da kuma yin ayyuka masu inganci da nagarta, musamman yadda yadda a sassan jihoshin Najeriya akwai ayyukan wannan kamfani.

Babban albishir din dai shine kamar yadda wannan kamfani yake kawo injina na musamman daga kasar China ko kuma a kirkiri injin a kamfanin na Afuwa Welding Works, to a wannan sabuwar shekarar ma za a zuba sababbin injina masu yin wani aikin na daban kuma na musamman.

Kamar yadda kuke ganin hoton wannan injin yana daga cikin sababbin injinan da wannan kamfani zai sanya domin ingantamuku ayyukanku.

Tabbas ko a haka ma dukkanin wanda ya ziyarci wannan kamfani zata yake tamkar a kasar China yake wajen fannin kere-kere ballantana ma kuma ace an zuba wadannan injinan da ake maganar kawo su.

Wannan kamfani dai kasar Najeriya ma tana alfahari da shi wajen kara fito da kimar kasar a idon duniya musamman yadda ake kawo aiki daga kasashen waje musamman daga Chad da Niger da Cameroon da Senegal da Togo kai harma daga kasar India.

Send:

Leave a Reply