Contact Info

Ga Saƙon Barka da Juma’a Daga Bakin Alh Mustapha A Sani Mammalakin Kamfanin Afuwa Welding Works & General Metal Construction

Kamar kowanne mako Shugaban katafaren wannan kamfani na sarrafa ƙarfe ya sake miƙa saƙon barka da Juma’a wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Wannan kamfani dai kamfanine da ya ƙware wajen yin ayyuka masu inganci da nagarta.

A wannan rana dai ta Juma’a Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’umma da cewa a yiwa iyaye biyayya domin mutum bashi da kamarsu.

“Kirana da zanyi a yau wato a wannan rana ta Juma’a muci gaba da kyautatawa iyayenmu, domin bamu da kamarsu, sabo da dukkanin wanda yake kyautatawa iyayensa a to tabbas zai zauna lafiya da kwanciyar hankali domin Allah da Annabi sunyimana nuni da mu kyautatawa iyayenmu”.

Daga ƙarshe Mustapha A Sani ya bayyana cewar dukkanin waɗanda iyayensu su ka rasu to suci gaba da yimusu addua.

Send:

Leave a Reply