Contact Info

Fasihin Engineer Wato Eng. Mustapha A Sani ya Sake Yin Amfani da Baiwarsa Wajen Hada Wani Sabon Injin Ayyukan Karfe.

 

Daga Amina Abdurrahman.

Fasihin Eng kuma shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works Eng. Mustapha A Sani ya sake amfani da baiwar da Allah yayimasa wajen kirkirar shimfidar injin yankan karfe.

Biyo bayan yadda muka saka wannan bayani da kuma bidiyo a shafukanmu na facebook da twitter yanzu kuma gashi a shafinmu na yanar gizo kamar yadda mabiya shafin daga kasashen duniya daban daban suke bibiyar shafin domin kallo da karantawa da kuma tofa albarkacin bakinsu.

Alhaji Mustapha A Sani ya sake kitkirar abinne biyo bayan yadda yaga kasar China tanayi a yunkurinsa na sake zuba sababbin injina a wani sabon bangare na musamman da aka sake kirkira.

Idan za a iya tunawa Eng. Mustapha A Sani ya taba kirkirar irin wannan gado a shekarar data gabata wato daya daga cikin injinan da suke aiki na CNC Plasma Cutting Machine wato Injin da akaga yana zana hoton mutane da yiwa karfe ado.

Wannan kamfani a kullum akan kirkira yake kamar yadda shugaban kamfanin yake fada ako da yaushe.

Wannan dai shine kan gadon Injin da aka kirkira kuma a kwanannan zaifata aiki biyo bayan yadda mukasakamuku kan Injin kuka ganshi a shaginmu na sada zumunta a kwanakinnan.

Haka zalika wannan kamfani a shirye yake domin ci gaba da kirkirar abunuwan da babu irinsa a kasarnan kamar yadda kasar China takeyi.

Wannan kamfani dai yanzu haka ana alfahari dashi a jihar Kano da Najeriya da Afrika baki daya biyo bayan yadda yake ayyuka masu inganci da nagarta.

Daga karshe zamuce kuci gaba da bibiyar wannan shafi namu na yanar gizo domin ganin labarai da dumi duminsu ako da yaushe.

Send:

Leave a Reply