Contact Info

Faɗakarwarmu ta Wannan Rana ta Juma’a Daga Bakin Mustapha A Sani Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction

Yau Juma’a, kamar kowanne mako ta wannan shafi na www.afuwaweldingworks.com ya kan bayar da sanarwa daga bakin mamallakin wannan kamfani akan nasiha da wa’azantarwa da faɗakarwa da sauransu.

A wannan rana Mustapha A Sani ya yi kira ga al’umma da su guji yin ha’inci wato su daina ha’intar junansu.

“Ina kira da yin nasiha ga mutane su daina ha’inci, domin yin ha’inci babu kyau, Allah S.W.A bayason zalunci, kuma ha’inci na daga cikin zalunci, sabo da haka mu gijewa yinsa”.

Alhaji Mustapha A Sani ya ƙara da cewar dukkanin mai yin ha’inci to abin yana dawowa zuwa kansa.

Daga ƙarshe Mustapha A Sani yayi addua’ar Allah ya sassautamana tsadar rayuwar da take damun ‘yan Najeriya da sauran sassan duniya.

Send:

Leave a Reply