Contact Info

Bayanai na Musamman Dangane da Ayyyuka Sama da Guda 100 da Injin Hydraulic Yake yi

BayBayanaianai na MusaMusammanmman Dangane da Ayuka Sama da Guda 100 da Injin Hydraulic Yake yi a Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction

 

Wannan ayyuka na karafuna da ku ke gani a zube a cikin kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction an yi su ne da shahararren injinnan da ake kira da suna Hydraulic Machine.

Wannan inji dai ana ganinsa ganin raina kama kaga gayaamma kuma ayyukan da yake gudanarwa yafi kala 100.

Masu karatu za su dinga tambayar kansu cewar ta yaya za a ce kamar wannan inji zaiyi ayyuka sama da kala dari amma ahakansa.

Wannan amsa dai shine sai mutum ya kasance a kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works zai ganewa idanunsa irin ayyukan da ake yi dashi abin zai bashi mamaki musamman.

Haka zalika da zarar shugaban kamfanin na Afuwa Welding Works wato Eng. Mustapha Abdullahi Sani ya hau kan injin yana aiki da shi to tabbas za ka ga abubuwan mamaki musamman idan yana yin bayanai dalla dalla a kansa tare da aiki a lokaci guda.

Wannan inji bashi kadai bane a kamfanin Afuwa Welding Works suna da yawa da adadinsu ba zai fadu ba, haka zalika ako wanne sashe na kamfanin akwai tarin injinan da yawa ta yadda idan mutum ta shiga zai zata a kamfanin kera injina yake ko kuma a kasar China yake.

Wannan kamfani na maraba da abokanan hulda wato kwastomomi daga sassan kasar Nijeriya dama sauran kwastomominsa na kasashen waje gami da jinjina a gare su.

Send:

Leave a Reply