Contact Info

Bayanan Yadda Ma’aikatan Kamfanin Afuwa Welding Works Suke Gudanar da Fenti da Zarar An Kammala Aiki.

Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.

Akowanne sashe na kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction akwai gogaggun ma’aikatan da ake sanyawa su gudanar da aikinsu.

Saidai kuma akwai ma’aikatan da sun kasance suna gudanar da aiki kala-kala kuma akowanne sashe aka kaisu.

Amma kuma kowanne akwai fannin da yafi kwarewa wajen gudanar da aikinsa.

Haka zalika shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works Eng. Mustapha A Sani ya kasance ya san yanayin kwarewar ma’aikatansa ta wajen yadda yake saka kowa aiki.

Wadannan masu gudanar da aikin fentin kamar yadda ake gani sun kasance aikinsu ne kuma su kan yi shi ya fita yadda akeso.

Haka zalika a wajen yin fentin kyamare ko fitilar kan titi nan ma akan sanya kwararrun abin a kamfanin domin gudanar da aikin fentin.

Kamar yadda ake gani wannan kalar fentin ja ne, kuma an gudanar da wannan fentin a karshen makon da ya gabata lokacin suna kan gudanar da aikin.

Send:

Leave a Reply