Contact Info

Bayanan Yadda Ma’aikata Kamfanin Afuwa Welding Works Suke Wasu Ayyukan Cikin Salo da Fasaha.

Shekarun baya sun kasance a ko wanne kamfani na walda ko sarrafa karfe ba a amfani da injina na zamani sosai wajen sarrafa karfe.

 

Amma yanzu da yake komai na tafiya da zamani wasu kamfanonin sun fara yin amfani da injinan zamani.

Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction na daya daga cikin manyan kamfanonuwan da suke sarrafa karfe, sai dai yanzu kuma shi wannan kamfani shine yake zuwa da injina kala kala da babu irinsu a wasu kamfanonuwa.

Kamar yadda shugaban kamfanin na Afuwa Welding Works yake fada wato Eng. Mustapha Abdullahi Sani cewa yanzu kashe 70% injina ne suke aiki a wannan kamfani wajen zane a jikin karfe ko huda karfe, yayin da kashe 30% kuma da hannu ake gudanar da ayyukan.

Kamar yadda kuke kallon Ma’aikacin kamfanin gasunan suna zuba aiki ka’in da na’in a gaban injin da ake kira da (Hydraulic Machine) wato injin da yake ayyuka sama da kala 100.

Wannan inji ya kasance na zamani kuma mai ayyukan ban mamaki kala-kala da sai mutum ya gani sannan zai kara tabbatar da hakan.

Su kuma ma’aikatan kamfanin sun kasance jajirtattu biyo bayan yadda suka samu horo na musamman a wajen shugaban kamfanin na Afuwa Welding Works wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

Hakance ta sanya ko wanne aiki suke gudanar da shi mai inganci da nagarta a dukkanin ayyukan cikin kamfani da kuma na wajen kamfani.

Send:

Leave a Reply