Contact Info

Bayanan Ingantattun Kayayyakin Ayyuka Dakuma Yadda Ma’aikatanmu Suke Sarrafa Injinan Kamfanin Afuwa Welding Works.

Gani ya kori ji dangane da maganar kayayyakin aiki a wannan katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Badan komai ba sai yadda ake ganin yadda ma’aikatan kamfanin suke sarrafa dukkanin wasu injina da kayayyakin aiki cikin kwarewa gami da salo.

Yanzu wannan injin da kuke ganin anzakuke kyaure daga karkashinsa ya kasance yana buga kyamare masu nagarta da inganci har sama da guda Dubu 1,000 a rana daya.

Wannan inji ya kasance ana sarrafa shi da na’ura mai kwakwalwa (computer) yayin gudanar da aiki.

Haka zalika suma wadannan tarin injina ne da guda daya acikinsu yanayin aiki kala-kala sama da guda 50.

Wannan kamfani dai ya kasance akwai injina da addinsu ba zai lissafu ba kuma kowanne da aikin da yake gudanarwa.

Haka zalika shima wannan injin da kuke ganin mutane guda biyu a kansa suna aiki a tare kuma suma cikin kwarewa da inganci kamar yadda ake ganinsu da kayan aikin kamfani a jikinsu.

Wadannan kadan daga cikin kayayyakin aikin wannan kamfani kenan da ake alfahari dashi a Kano da Najeriya dama Afrika baki daya wajen sarrafa karfe da yimasa yadda aka ga dama.

Send:

Leave a Reply