Contact Info

Bayanan Gani ya Kori ji kan yadda daya daga cikin manyan injinan sarrafa karfe yake yin ayyukansa maibtafiya da zamani da Kuma Yadda Za a Sake Zuba Sababbin Injina..

Kamar yadda komai ake tafiya da zamani to kamfanin Afuwa Welding Works shima cikin zamani yake tafiyar da aikinsa.

Wadannan sune hotunan ayyukan katafaren injinnan mai suna CNC Plasma Cutting Machine cikin tsari mai kyau.

Kamar yadda muke gaamuku kuma muke sake maimitamuku cewa wannan inji yana fitar da zane kala-kala har sama da kala dubu.

Haka zalika wannan inji da kuke gani dashi ake zana hoton mutane kamar yadda a kwanakin baya akafara zana hotunan wasu mashahuran ‘yan siyasa.

A iya injina masu yawa da kamfanin Afuwa Welding Works yake dasu masu tarin yawa shi kalar wannan injin mai suna CNC Plasma Cutting Machine guda biyu (2) ne, inda Eng. Mustapha A Sani ya siyo guda daya (1) daga kasar China sannan kuma yayi amfani da basirarsa ya kirkiri guda daya (1) da kansa a kamfanin nasa.

A yanzu haka injinan masu aiki kala daya guda biyu ne a kamfanin nasa na Afuwa Welding Works.

 

A yanzu kuma hoton wannan waje da kuke gani mai fitilu sabon waje ne da ake ci gaba da kawata shi da kuma gina shi ta yadda za a sanya sababbin injina da za a kawosu daga kasar China.

Engineer Mustapha A Sani dai ya kasance mai kirkirar abubuwa kala-kala biyo bayan yadda ya kirkiri injina da dama a kamfanin nasa.

Send:

Leave a Reply