Contact Info

Bayanan Aikin da Kamfanin Afuwa Welding Works ya Gudanar a Kamfanin Mai na Kasa Reshen Jihar Kano (NNPC).

Bayanan Aikin da Kamfanin Afuwa Welding Works ya Gudanar a Kamfanin Mai na Kasa Reshen Jihar Kano (NNPC)

 

Kamar yadda muke ci gaba da bayyanamuku ayyukan kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar a sassan kasar Najeriya da na kasashen waje ta cikin wannan shafi na yanar gizo da kuma sauran shafukan kamfanin na sada zumunta.

Yau alkalamin namu ya yi dirar mikiya a jihar Kano kuma a kamfanin mai na kasa reshen jihar Kano (NNPC).

Domin kuwa wannan kamfani ya gudanar da aiki a wannan waje kamar yadda ya saba gudanar da ayyuka a gurare daban-daban a sassan kasar Najeriya.

Kamar yadda ake ganin ma’aikatan kamfanin g su nan a lokacin da suke gudanar da wannan aiki a shekarun baya.

Ako da yaushe mukan bayyanamuku cewar wannan kamfani ya kan yi ayyukansa masu karko da nagarta gami da inganci.

To wannan aiki tunda kamfanin Afuwa Welding Works ya yishi har yanzu yananan daram babu alamar wata baraka a tattare da shi sabo da yadda akayi aikin cikin kwarewa da salon zamani.

Kuma muna sanarmuku da cewar wannan kamfani ya shirya zuwarmuku da salon ayyuka na musamman a wannan (sabuwar shekarar da muka shigo ta 2024.

Send:

Leave a Reply