Contact Info

Bayanai na Musamman Kan Yadda Motocin Kamfanin Afuwa Welding Works Suke Daukar Kayan Aikin Raftar Karfe Zuwa Sassan Kasar Najeriya da Zarar Anbaiwa Kamfanin Kwangilar Aiki.

Kamar yadda a farkon watan Janairu mu ka kawomuku labari da jawabin yadda motocin kamfanin Afuwa Welding Works su ke daukar fitilun kan titi suna kaisu jihoshi domin sakawa.

To a wannan rana ma munzomuku da jawabin yadda motocin su ke kai kayayyakin raftar karfe (metal rafter equipment).

Kamar yadda ake gani ga yadda motocin su ke dakko kayayyakin nan har zuwa jihoshi ko wajen da ake gudanar da wannan ayyuka.

Haka zalika daga cikin hotunan za a ga yadd wata mota ta tsaya cak ake sauke kayan aikin bayan isowarta waje ajiye kayan.

Sannan kuma wani lokacin ana gudanar da aikin tare da motar domin kamar yadda ake ganin motocin kamfanin guda 3 a wani hoto daga cikin hotunan ga wata mota nan ana gudanar da aikin tana mika kayan aikin zuwa ga mutanen da su ke yin aikin.

Wannan salon aikin dalla-dalla haka baya rasa nasaba da yadda fasihin shugaban kamfanin wato Eng. Mustapha A Sani ya tsaya tsyin daka wajen yin aiki cikin gakiya da rikon amana da kuma yiwa kwastomomi ayyuka masu nagarta da inganci.

Sannan irin wannan nagartar aiki ne ya sanya kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction zama zakaran gwajin dafi a dukkanin kmfanonin da su ke a kasar Najeriya da kuma samun yabo daga sassan kasar nan da ma duniya baki daya.

Send:

Leave a Reply